Gwamna Bala Mohammed Ya Kaddamar Da Aikin Sabunta Majalisar Dokokin Bauchi a Kan Naira Biliyan 7.8

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya kaddamar da aikin sabuntawa da gyaran ginin majalisar dokokin jihar a kan kudi Naira biliyan 7.8.

A yayin bikin kaddamarwar a ranar Talata, gwamnan ya ce wannan mataki yana nuna yadda gwamnatinsa ke kokarin samar da ingantaccen yanayi ga dukkan bangarorin mulki.

Ya bayyana cewa rabin kudin aikin an riga an biya kamfanin da ke aiwatar da shi, kuma an tsara aikin zai kammala cikin shekara guda.

Shima da yake jawabi, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, ya ce tun bayan ginin majalisar a zamanin marigayi Gwamna Abubakar Tatari-Ali a shekarun 1980, sai dai karamin gyara da aka yi a 2011.

Ya ce gyaran zai kawo sabuntawa ga dakin taro da ofisoshi, da kuma kara inganta ayyukan majalisar wajen wakiltar al’umma.

Kwamishinan Gidaje da Muhalli, Danlami Kaule, ya ce ma’aikatarsa za ta sa ido sosai don tabbatar da cewa aikin ya gudana kamar yadda aka tsara tare da inganci.

More from this stream

Recomended