Gwamna Malam Umar A. Namadi ya amince da nadin Farfesa Muhammad Ibrahim Yakasai a matsayin sabon shugaban jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa, SLU.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim ya sanya wa hannu. .
Sanarwar ta ce nadin sabon shugaban jami’ar ya biyo bayan shawarwarin da majalisar gudanarwar jami’ar ta bayar kamar yadda dokar da ta kafa jami’ar ta tanada.