Gobarar Siyasa Na Kara Ruruwa A Nigeria

Gobarar siyasar dake ci a na Nigeria yanzu ta na kara ruruwa ganin yadda wasu jigajigan ‘yan siyasa da suka fice daga jam’iyyar PDP suke sukar jam’iyyar APC mai mulki musamman a wannan lokacin da ake yawan rikici a zabukan fitar da ‘yan takarar ita jam’iyyar APC din.

Wadanda suka fice daga PDP na ikirarin sun yi hakan ne da zummar damarar kwace mulki daga hannun shugaba Muhammad Buhari na jam’iyyar APC.

Tsohon kakakin jam’iyyar PDP wanda yanzu shi ne shugaban kwamitin taron kasa na jam’iyyar SDP Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali ya bayyana manufofinsu. A cewarsa duk lokacin da kasa ta kama hanyar lalacewa Allah yak an kawo wata hanyar gyara.

Parfessa Alkali yace su da suka fice daga PDP suka kafa jam’iyyar SDP, sun yi hakan ne saboda tabarbarewar abubuwa. Burinsu yace shine gyara dazarar suka kama iko.

Sai dai ministan harkokin matasa da wasanni Barrister Solomon Dalung ya ce akwai dalilin da ya sa wasu ‘yan siyasa ke adawa da shugaba Buhari. Ya ce laifin Buhari daya ne. “Ana cin abinci a cikin duhu ya je ya haska wuta” A cewarsa ba karamin bashi gwamnatin Buhari ta tarar ba, amma yanzu an rage.har ma an boye wasu kudi wajen ajiya. Babu wanda ya san an boyesu. Ya ce kafa TSA, wato ajiye duk kudaden gwamnati cikin asusu daya ya hana yashe dukiyar jama’a, hakan Mr Dalung ya ci gaba d a cewa, ya hana watanda da kudin gwamnati kamar yadda ake yi da can. Ya ce Buhari ya daura damarar yaki da kowa sai ya mayarwa Nigeria arzikinta da aka wawure.

More News

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...