Rahotannin fa ke fitowa daga Arewacin Najeriya na nuna cewa Allah ya yi wa tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya Ghali Umar Na’Abba rasuwa.
Bayanai daga iyalansa sun ce ya rasu ne yau da asuba bayan ya yi fama da jinya a Abuja, babban birnin kasar.
An haife shi a birnin Kano a shekarar 1958.