Gwamnatin Jihar Kogi ta tabbatar da cewa fursunoni 12 sun tsere daga gidan yari na tarayya da ke Kotonkarfe da safiyar Litinin.
Kwamishinan Watsa Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo, ya fitar da sanarwa yana yabawa hukumomin tsaro bisa gaggawar daukar matakin da suka yi bayan faruwar lamarin.
Fanwo ya bayyana harin a matsayin abin takaici, inda ya tabbatar da cewa gwamnati na daukar matakan da suka dace don hana irin haka nan gaba.
A cewarsa, gwamnati za ta hada kai da hukumomin tsaro domin gano yadda lamarin ya faru.
Fursunoni 12 Sun Tsere Daga Gidan Yari a Kogi
