Fubara Ya Karɓi Mulki A Jihar Rivers Bayan Ƙarewar Dokar Ta-Baci

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya koma kan kujerarsa bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗaga dokar ta-baci da aka shimfiɗa a jihar tsawon watanni shida.

Rear Admiral Ibok-Ete Ibas, wanda ya yi aiki a matsayin Sole Administrator a lokacin dokar ta-bacin, ya mika ragamar mulki ga Fubara tare da yin jawabi na bankwana ga al’ummar jihar.

Ya kuma bayyana cewa an dawo da doka da oda, an gudanar da zaɓen kananan hukumomi, sannan aka kafa hukumomi da kwamitocin gwamnati da ke aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata.

Fubara dai ya koma ofis a hukumance, inda ake sa ran zai ci gaba da gudanar da ayyukansa a matsayin zababben gwamnan jihar.

More from this stream

Recomended