Fitacciyar ma’aikaciyar rediyo Tosyn Bucknor ta rasu

Tosin Bucknor

Oluwatosin ‘Tosyn’ Bucknor, fitacciyar mai gabatar da shirye-shirye a gidan rediyon Inspiration FM, ta rasu tana da shekara 37, in ji rahoton da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya bayar.

Mijin matashiyar, wacce aka fi sani da Tosyn, Aurelien Boyer ne ya gano gawar matar tasa ranar Litinin da daddare lokacin da ya koma gida daga wurin aiki.

NAN ya kara da cewa “An haifi Tosyn, wacce ta yi digirinta a fannin shari’a na Jami’ar Lagos, sickle cell anaemia, shi ya sa ta rika gabatar da shiri mai suna These Genes Project domin taimakawa masu fama da cutar.”

An daura auren Boyer, wanda dan kasar Fransa ne da Tosin a watan Nuwamba na 2015 a birnin Lagos da kuma kasar Faransa.

A baya dai Tosyn ta rika gabatar da wani shirin safe a Top Radio FM.

Ta soma aikin gabatar da shirye-shiryen rediyo mai suna Tee-A a Eko FM. Ta yi aikin samun horo a Cool FM inda ta rika gabatar da shirin the Fun Hour Show ranar Asabar.

Tosyn ta fara aiki da Top Radio bayan ta kammala hidimar kasa a 2009 inda ta kasance mace ta farko da ta rika gabatar da shirin safe.

‘Yan Najeriya da dama, musamman masu amfani da shafukan sada zumunta, sun bayyana alhininsu bisa rasuwar ‘Tosyn’ Bucknor.

More from this stream

Recomended