Fitaccen malamin addinin Islama daga Jihar Bauchi, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, ya riga mu gidan gaskiya.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a gidansa da ke Bauchi, inda ake sa ran gudanar da jana’izarsa a safiyar yau Juma’a.
Dokta Idris ya dade yana fama da rashin lafiya, lamarin da ya sa gabanin watan Ramadana ya tafi kasashen Masar da Saudiyya domin neman magani.
A fitowarsa ta karshe da aka gani a bainar jama’a, ya gabatar da huduba a ranar Idin Karamar Sallah da ta gabata, inda ya jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin Musulmi.
Marigayin ya kasance malami mai fada a ji wanda ya yi tasiri a harkokin addini, kuma ya bar tarihi mai kyau a fagen wa’azi da karantarwa.
Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa kura-kuransa, amin.
Fitaccen Malamin Addini Dokta Idris Dutsen Tanshi Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
