Fasto ya nemi afuwa bisa latsa maman mawakiya Ariana Grande

[ad_1]

Ariana Grande at Aretha Franklin's funeral

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Limanin cocin da ya jagoranci jana’izar mawakiya Aretha Franklin ya nemi afuwar shahararriyar mawakiyar nan Ariana Grande bayan da aka zarge shi da latsa mamanta a kan dandamali.

Hotuna sun nuna Bishop Charles H Ellis III ya rike kugun Ariana inda dan yatsansa ya rika latsa mamanta.

Sai dai ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na the Associated Press cewa “ba ni da niyyar taba maman ko wacce mace.”

“Watakila na wuce gona da iri, watakila kuma na nuna matukar abota da shakuwa, amma ina neman afuwa,” in ji shi.

Malamin cocin ya ce yana rungumar dukkan mawaka, maza da mata, a lokutan bukukuwa.

Sai dai mutanen da suka kalli jana’izar a talbijin sun rika wallafa hotuna lokacin da Ariana ta mike tsaye domin rera wakar Aretha msai suna (You Make Me Feel Like) A Natural Woman.

Mutane da dama na ganin Bishop Ellis ya yi azarbabin sanya hannunsa inda bai dace ba lokacin da yake magana da mawakiyar mai shekara 25 – suna masu cewa da alama ba ta ji dadin yadda ya rike jikinta ba.

Kazalika wasu sun soki Ariana saboda sanya tufafin da ba su dace ba zuwa coci, suna masu cewa tufafin dangalallu ne.

[ad_2]

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...