
Mataimakin shugaban kasa,Yemi Osinbajo ya ce farashin man fetur zai iya kai wa ₦220 ko kuma sama da haka matukar gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur.
Osibanjo ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin muhawara a tsakanin yan takarar mataimakin shugaban kasar.
Ya ce gwamnati baza ta iya cire tallafin ba saboda illar da hakan zai haifar ga rayuwar yan Najeriya.
Osibanjo ya bayyana cewa kamfanin NNPC ne kamfani daya tilo dake shigo da man fetur saboda haka daga cikin asusunsu ake biyan tallafin man.
“Yanzu, bari na fada maka idan yau muka cire tallafi farashin litar mai zai iya kaiwa ₦220 ko kuma sama da haka,”ya ce.