Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru El-Rufai ya kai ziyarar ta’aziya ga iyalan Agom Adara mai martaba Maiwada Raphael Galadima wanda masu garkuwa da mutane suka kashe a makon da ya wuce.
Ya yin ziyarar gwamnan na tare da mataimakin sa, Barnabas Bala.
An dai yi garkuwa da marigyin tare da mai dakinsa da kuma wasu mutane uku.
Mutane da dama sun bayyana marigayin a matsayin mutum mai son zaman lafiya.