Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, ya yi afuwa ga fursunoni goma da ke tsare a cibiyoyin gyaran hali daban-daban a fadin jihar.
A cewar sanarwar da Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Jihar, Bello Abdulkadir Fanini, ya fitar ga manema labarai, wannan afuwa na da nufin bai wa wadanda suka ci gajiyarta damar sake haduwa da iyalansu a lokacin azumin Ramadan da bikin Eid-el-Fitr.
Sanarwar ta bayyana cewa afuwar da aka yi wa fursunonin ta biyo bayan shawarar da Majalisar Shawara kan Hakkin Afuwa ta Jihar ta bayar, bisa tanadin sashe na 212 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999.
Eid-el-Fitr: Gwamnan Jigawa Ya Yi Afuwa Ga Fursunoni 10
