EFCC zata saka idanu kan kudaden yakin neman zaben 2019

Ibrahim Magu,shugaban hukumar EFCC dake Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ya ce hukumar za ta saka idanu wajen bin diddigin kudaden yakin neman zaben jam’iyun siyasa a zaben shekarar 2019.

Haka kuma hukumar zata saka ido kan kudaden gudunmawa da kuma mutanen da suka bayar.

Magu ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wata takarda a wurin taron kana rawa juna sani da aka shirya gwamnoni 36 na kasarnan da kuma manyan masu ruwa da tsaki akan harkar zaɓe.

Shugaban na EFCC wanda ya samu wakilicin shugaban ma’aikatansa, Olanipekun Olukoyede ya ce hukumar ba za tabari a karkatar da kuɗaɗen al’umma ba wajen daukar nauyin yakin neman zabe.

Ya ce ana bukatar yan siyasa su ajiye bayanan dukkanin wata gudunmawa da suka karba da kuma bayanan mutanen da suka bayar domin nunawa jami’an tsaro a duk lokacin da aka bukaci haka bayan an kammala zabe.

Yan Najeriya da dama sun dade suna zargin shugabanni da karkatar da kuɗaɗen jama’a wajen yakin neman zabe. Abin jira a gani shine ko wannan yunkurin na EFCC zai kawo karshen karkatar da kudaden.

More from this stream

Recomended