EFCC ta kama ‘yan China kan yunkurin bai wa jami’inta cin hanci | BBC News

.

Hakkin mallakar hoto
@officialEFCC

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC, ta ce ta kama wasu ‘yan kasar China biyu bisa zargin bai wa jami’inta cin hanci.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya fitar ranar Talata ta ce jami’anta sun kama Mr. Meng Wei Kun da Mr. Xu Koi a Sokoto bisa laifin bai wa shugabanta reshen jihar Mr. Abdullahi Lawal, cin hancin N50m.

A cewar EFCC, mutanen biyu sun bayar da cin hancin ne domin su hana binciken da ake gudanarwa kan kamfanin gine-gine na China Zhonghao Nig. Ltd, wanda gwamnatin jihar Zamfara ta bai wa kwangilar da ta kai N50bi tsakanin shekarar 2012 zuwa 2019.

Shugaban hukumar reshen jihar Sokoto yana binciken kamfanin ne game da aiwatar da kwangilolin gina hanyoyi a garuruwan Gummi, Bukkuyun, Anka da kuma Nassarawa da ke jihar ta Zamfara; a da kuma haƙa rijiyoyi 168 masu amfani da hasken rana a kananan hukumomi 14.

EFCC ta ce ‘yan kasar ta China sun razana ne saboda yadda suka ga shugaban hukumar reshen jihar ta Sokoto tana gudanar da aikinsa ba sani ba saboda, abin da ya sa suka nemi ba shi cin hancin N100m.

Daga nan ne, Mr Lawal ya yi musu ƙofar-rago inda ranar Litinin wakilan kamfanin biyu Meng Wei Kun da Xu Kuoi suka ba shi N50m a kan hanyar filin jirgin saman Sokoto a matsayin kashin farko na cin hancin.

Sun yi alkawarin bashi ragowar N50m daga bisani.

Sai dai EFCC ta ce nan take aka kama mutanen biyu da kudin da suka bayar wadanda za a yi amfani da su a matsayin shaida a gaban kotu.

EFCC ta soma binciken kamfanin ne bayan da a cewar ta, bayanan sirri suka nuna cewa an yi almubazzaranci da kudin da kuma halasta kudaden haramun lokacin bayar da kwangilar.

Binciken ya gano cewa kamfanin na China Zounghao Ltd ya karbi N41b daga gwamnatin jihar Zamfara kuma ya karkatar da N16b.

Hukumar ta EFCC ta ce nan gaba kadan za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu.

More from this stream

Recomended