Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), reshen Ilorin, ta kama mutum 47 da ake zargi da aikata zamba ta yanar gizo a wani samame da aka kai a sassa daban-daban na jihar Kwara a ranar Alhamis.
A wata sanarwa da sashen yada labarai na hukumar ya fitar, an bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne a wurare masu muhimmanci ciki har da titin Awolowo, unguwar Tanke, Harmony Estate a Ilorin, da kuma garuruwan Ganmo da Amoyo a karamar hukumar Ifelodun ta jihar.
Hukumar ta ce an kama su ne bisa sahihan bayanan sirri da aka tattara dangane da rawar da suka taka wajen aikata laifukan zamba iri-iri ta kafar intanet.
Kayan da aka gano a wajen wadanda ake zargin sun hada da motocin alfarma guda 10, wayoyi kirar zamani daban-daban guda 74, kwamfutocin tafi-da-gidanka guda 18 da kuma babur guda daya – wadanda ake kyautata zaton kudin sata ne aka saya da su.
EFCC ta ce za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.
EFCC Ta Kama Mutum 47 Bisa Zargin Zamba Ta Intanet a Jihar Kwara
