Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kama Akanta-Janar na Jihar Bauchi, Sirajo Jaja, bisa zargin almundahana da kudaden gwamnati da suka kai naira biliyan 70.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta bayyana cewa an kama Jaja ne tare da wasu mutane biyu – Aliyu Abubakar, wanda ake zargi da gudanar da haramtacciyar hada-hadar kudade ta hanyar BDC, da kuma Sunusi Ibrahim Sambo, mai gudanar da hada-hadar kudi ta hanyar PoS.
Hukumar EFCC ta ce binciken da take yi ya nuna cewa an fitar da sama da naira biliyan 59 daga asusun banki daban-daban da ke karkashin ikon Akanta-Janar din, inda daga baya aka mika kudaden ga Aliyu Abubakar da Sunusi Ibrahim Sambo. Wadannan mutane, a cewar EFCC, sun rabawa wakilan jam’iyya da wasu abokan hulda na Gwamna Bala Mohammed kudaden.
Baya ga haka, hukumar ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan Gwamna Bala Mohammed dangane da wannan badakala.
Kakakin EFCC ya kuma ce Aliyu Abubakar, wanda a baya ya tsere bayan an bada belinsa, yanzu an sake cafke shi.
“Hukumar tana kokarin bin diddigin kudaden da aka karkatar, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci mai tsanani,” in ji Oyewale.
A halin yanzu, EFCC ta ce bincike na ci gaba, sannan wadanda ake zargin na nan a tsare don karin tambayoyi.
EFCC Ta Kama Akanta-Janar na Jihar Bauchi Bisa Zargin Satar Naira Biliyan 70
