
Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annat ta yi ikirarin cewa jami’anta sun kama gwala-gwalai da farashinsu ya kai N211m a filin jirgin saman Lagos.
Wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC, Mr Tony Orilade, ya aike wa manema labarai ta ce an yi niyyar kai gwala-gwalan be birnin Dubai.
A cewar Mr Orilade, an kama mutumin da ke dauke da zinaren kuma tuni jami’an hukumar suka tsare shi.
- An daure Malamin ‘tsubbu’ kan kudin jabu a Kano
- Shin Buhari zai cire Ibrahim Magu?
“Sakamakon bayanan sirrin da muka samu, ranar tara ga watan Nuwamba, 2018 jami’anmu sun gano gwala-gwalai mai nauyin kilogiram 35 a hanyar shiga jirgi ta filin jirgin saman Lagos kuma yanzu EFCC na tsare da mutumin da ke dauke da gwala-gwalan.”
Yanzu haka ana gudanar da binci domin gano wadanda ke da hannu wajen yunkurin fitar da wadannan gwala-gwalai ba bisa ka’ida ba ko da yake mutumin da aka kama yana bai wa jami’anmu hadin kai wurin bincike, in ji EFCC.
A watan Maris na 2017 ma EFCC ta kama wadansu jakuna dauke da zinaren da ya kai N49 a filin jirgin saman Kaduna inda ake shirin fitar da shi daga kasar.