EFCC ta bankado wasu gidaje mallakin Fayose

Hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFFC ta wallafa wasu hotunan gidaje da take zargin tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya saya da kudaden haram

Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar shi ne ya saki hotunan gidaje ranar Laraba, ya ce an gano gidajen lokacin da hukumar take bincike kan zargin aikata cin hanci da rashawa da a kewa tsohon gwamnan.

Uwujaren ya yi zargin cewa Fayose ya sayi gidajen ne da kudin da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro Kanal Sambo Dasuki ya bashi.

“A binciken da muke na zargin aikata cin hanci da rashawa kan tsohon gwamna Fayose musamman kan kudi biliyan ₦1.3 da ya karba daga ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro.Hukumar ta bankado wasu hujjoji dake nuna cewa ya karkatar da kudade wajen sayen wasu gidaje a unguwanni masu daraja dake birnin tarayya Abuja,”Wilson ya ce.

A ranar Talata ne dai Fayose ya kai kansa ofishin hukumar dake Abuja dai-dai lokacin da ake rantsar Kayode Fayemi a matsayin sabon gwamnan jihar.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...