‘Duniya tana kallon ku’ Buhari ya fadawa yan majalisar kasa masu yi masa ihu

A kokarinsa na shawo kan yan majalisar kasa dake masa ihu yayin da yake jawabin kasafin kudin shekarar 2019, shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce baki dayan duniya na kallon abinda yake faruwa.

Yan majalisar sun katse jawabin shugaban kasar inda suka ce “farfaganda, karya ce”.

An yi masa ihu lokacin da yafara jawabi kan nasarorin gwamnatinsa da farko shugaban ya nuna nutsuwa amma fusatattun yan majalisar suka cigaba da yi masa katsalandan.

A wannan gabar ne shugaban ya ce ” Zan yi roko ga mambobin wannan majalisa masu girma cewa duniya fa tana kallon mu ya kamata ace mun wuce haka.”

Mai makon su amince da rokon shugaban kasar fusatattun yan majalisar sun cigaba da yi masa ihu

More from this stream

Recomended