Dole mu nemi hakkinmu a Kotu – Gwamnatin Kano

Gwamnan Kano Umar Ganduje tare da dan jarida Ja'afar da ya saki hutunan bidiyo


Gwamnan Kano Umar Ganduje tare da dan jarida Ja’afar da ya saki hutunan bidiyo

Gwamnatin Jihar Kano ta ce dole ne ta nemi hakkinta a kotu kan dan jaridar da ya saki hutunan bidiyo da ke nuna gwamna Abdullahi Ganduje na karbar rashawar miliyoyin dala.

Gwamnatin ta ce za ta gurfanar dan jarida Ja’afar Ja’afar a gaban kuliya duk da majalisar jihar ta kafa kwamitin tantance sahihancin hutunan bidiyon da ya saki.

Gwamnatin ta bayyana cewa idan majalisar dokoki za ta iya ladabtar da gwamna, ba ta da hurumin ladabtar da dan jaridar.

Mai bai wa gwamnan na Kano shawara kan harkokin siyasa Alhaji Mustapha Buhari Bakwana ya shaidawa BBC cewa wannan zargi ne da ke da nasaba da zagon-kasa irin na siyasa.

“Abokan adawa ne wadanda ba su bukatar wannan gwamnati da ke yaki da cin hanci da rashawa, shi ne aka fara hada wannan sharrin” in ji shi.

Ya kuma ce don an ga irin yawan kuri’un da gwamna ya ba shugaban kasa a zaben fitar da gwani, shi ya sa aka fara yin zagon-kasa don kada ya samu nasara.

A makon da ya gabata ne jaridar Daily Nigerian da ke wallafa labaranta a intanet ta saki labarin cewa wani gwamna a yankin arewa maso yammacin kasar wanda ke neman zarcewa a mulki karo na biyu, yana karbar makudan kudade a wajen wasu ‘yan kwangila.

Daga baya kuma mawallafin jaridar Ja’afar Ja’afar ya saki hutunan bidiyo guda biyu daga cikin 15 da ya ce yana da su a hannu.

A cikin hutunan bidiyon an nuna gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yana karbar miliyoyin dala daga hannun wani da aka ce dan kwangila ne, zargin da gwamnatin Kano ta musanta.

Tun bayan buga labarin ne dai, dan jaridar Ja’afar Ja’afar ya ce ana yi wa rayuwarsa barazana.

A ranar Litinin din da ta gabata ne majalisar dokokin jihar ta kafa kwamitin da zai gudanar da bincike a kan zargin, inda ta bukaci bangaren zartarwa da ya jingine maganar shari`a.

Hotunan bidiyon da ake zargin gwamnan na Kano da rashawa na ci gaba da jan hankali a shafukan intanet kuma lamarin da ke ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...