Dan Najeriyar da ke biya wa mutane kudin asibiti a asirce

Kashi biyar din 'yan Najeriya ne kawai ke da insorar lafiya

Kashi biyar din ‘yan Najeriya ne kawai ke da insorar lafiya

A Najeriya ayyukan da ake yi wa mutane a asibiti kadan ne ake yi kyauta, wasu lokutan ko majinyaci ya biya ana iya hana ka tafiya daga asibitin.

Zeal Akaraiwai, wani matashi ne dan shekara 40 kuma kwararre ne a harkar tattalin arziki.

Mutum ne wanda ke biya wa marassa lafiya kudin asibiti kyauta a kasar.

Yana shiga asibitoci inda yake haduwa da ma’aikatan lafiya domin su bashi jerin sunayen mutanen da zai biya wa kudin asibiti.

Ma’aikatan lafiyan suna kai Zeal zuwa gadajen masu fama da rashin lafiya inda yake tattaunawa da su.

Wani matashi mai aski ya bayyana masa cewa an harbe shi da bindiga ne babu gaira babu dalili.

“Ta ya ya zaka biya kudaden asibitin naka?” Zeal ya tambaye shi.

”Ina ta addua ne kawai” mutumin ya amsa wa Zeal.

Zeal kwararre ne a ilimin tattalin arziki

Sun tattauna da Zeal – bai tambayi Zeal kowanene shi ba, shi kuma bai fada masa ba.

Daga baya sai Zeal ya duba kudaden asibitin matashin tare da wata Nas, kudin da ya kai Dala 250.

Mai askin yayi sa’a, Zeal zai biya kudin asibitin.

Zeal ba ya sake haduwa da wadanda ya biya kudin asibitinsu, ba ya ma son su gode masa.

Amma yana so su bada labarinsa, na yadda wani mutum ya zo ya cece su ya biya masu kudaden asibiti.

Yana biya wa mutane wadanda ke da yiyuwar rayuwa ne domin su koma gidajensu
A sashen mata Zeal ya je wajen wata ‘yar shekara 60 wacca ba ta cikin hayyacinta.

Tana fama ne da ciwon zuciya.

Zeal ya biya kudaden da aka kashe mata tun kawo ta asibitin, domin a samu damar kai ta sashen da zata samu kulawa ta musamman.

Zeal yana aje bayanan duka mutanen da ya taimakawa a wani bakin littafi.

Ya kuma tuna da Montserrat – matar da aka tsare wata 11 a asbibiti saboda an yi mata tiyatar cire mahaifarta, Zeal ya biya mata Dala 400 na kudin aikin.

Taimakon da Zeal yake bayarwa yana sanya shi farin ciki, amma yana matukar bakin ciki a kan gazawar gwamnati.


Zeal ne ya kafa wannan gidauniya inda yake aiki tare da wasu Nas

A Najeriya, kashi biyar na ‘yan kasar ne kawai ke da inshorar lafiya.

Akwai rudani sosai a kan yadda tsarin lafiya na bai daya zai yi aiki, ganin cewa akwai gibi sosai na kudaden da masu hali ke biya da karancin kudaden da marassa karfi ke biya – wanda gwamnati ke cika masu.

Amma Zeal ba zai iya hakuri ba.

”A kowanne mako ina ganin illar rashin samar da inshorar lafiya ta dole, mutane na mutuwa. Toh menene farashin rayuwar dan adam?”

More from this stream

Recomended