
Gabanin zuwansa Najeriya, Yarima Charles ya ziyarci Ghana da Gambia
Dan gidan sarauniyar Ingila mai jiran gadon sarautar Birtaniya, Yarima Charles yana ziyara a Najeriya ranar Talata.
Basaraken ya sauka a Abuja, fadar gwamnatin kasar inda yake ganawa da mahukuntan Najeriya da sarakuna da shugabannin al’umma.
Sanarwar da tawagarsa ta fitar ta nuna cewa yariman zai kai ziyara Lagos bayan ya kammala wadda yake yi a Abuja.
- Ko ‘yan Najeriya za su iya aikin soja a Birtaniya?
- An nada ministar yaki da kunar bakin wake a Birtaniya
Tun da fari dai an shirya zai kai irin wannan ziyara Jos, babban birnin jihar Filato amma daga bisani aka soke ziyarar sakamakon shawarar da ofishin jakadancin Burtaniya da ke Najeriya ya ba shi.
Da ma dai an sa ran zai gabatar da jawabi a Jos kan yadda za a magance rikice-rikicen kabilanci da addini wadanda birnin ya sha fama da su.
Gabanin zuwansa Najeriya, Yarima Charles ya ziyarci Ghana da Gambia