
Ministan harkokin sadarwa Adebayo Shittu ya yin karin haske kan dalilin da yasa shi rufe Ofishin yaƙin neman zaben shugaban kasa Muhammad Buhari na shiyar kudu maso yammacin kasarnan.
Wasu rahotanni dake yawo a gari sun bayyana cewa ministan ya dakatar da yakin neman zaben shugaban kasa Muhammad Buhari biyo bayan hana shi takarar gwamnan jihar Oyo da da jam’iyar APC tayi.
Ministan ya ce rahotanni dake cewa ya dakatar da yiwa Buhari yakin neman zabe ba gaskiya bane ka wai bata sunansa ake son yi.
Ya ce ofishin yakin neman zaben gini ne na haya ba mallakinsa ba.
Shitu ya fadawa jaridar The Nation cewa ya karbi hayar ginin ofishin ne kan kudi miliyan ₦3 duk shekara kuma a yanzu ba zai iya cigaba da biyan kudin ba hakan ya jawo rufe Ofishin.
Ya kara da cewa har yanzu yana cikin jam’iyar APC da kuma gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.