Dakarun Najeriya Sun Dukufa Wajen Gano Gawar Janar Idris Alkali

Dakarun Najeriya, karkashin jagorancin Garizon kwamanda, runduna ta uku dake birnin Jos, Birgediya Janar Ibrahim Muhammad, ya ce binciken da suka fara gudanarwa na nuni da cewar an gano motar Janar Idris Alkali a yankin Dura Du, a karamar hukumar Jos ta Kudu, don haka suka fara yasar wani tafki da suke zaton an jefa motar Janar din.

Janar Muhammad, ya ce sun shafe mako guda kenan suna neman gawar Janar Idris Alkali, da motarsa Toyota Corolla, baka. Ya kara da cewamuna so mu san ko yana raye, wannan bincike da mukeyi na ceto, mun samu bayanai ne cewa an tura wadansu motoci a cikin rafin”.

Yace tun kwana uku kenan muke kokarin ganin ko zamu gano wani abu a cikin rafin amma ganin yadda rafin ya kasance tsohon wurin hakar ma’adinai ne ya kasance da wahala, duk da shike mun yi amfani da babbar motar dake daga abu mai nauyi amma har yanzu bamu gano shi ba. Janar Ibrahim Muhammad ya ce a yanzu haka sun yanke shawarar zasu janye ruwa daga rafin don gano abinda ke karkashin sa.

Janar Muhammad, ya hori al’ummar dake zaune a yankin da su basu hadin kai wajen bankado bata gari a jahar Pilato, ya kuma basu tabbacin jami’an tsaro ba zasu ci mutuncin kowa a yankin ba.

A halin da ake ciki kuma, yayinda sojojin ke yashe tafkin, mata saye da bakaken tufafi sun gudanar da zanga-zanga, wanda a cewarsu ruwan rafin suke amfani dashi yau da kullum. Jagorar matan, Mary Yakubu, ta ce in an yashe ruwan rafinya’yan su da mazajensu zasu mutu saboda haka basa son kowa ya taba ruwan.

A yanzu haka dai sojojin sun tsaurara matakan tsaro a yankin suna kuma gudanar da aikin yasar tafkin don gano gawar Janar Idris Alkali ko akasin haka.

More from this stream

Recomended