Da gaske Maryam Booth za ta auri Sadiq Zazzabi?

Maryam Booth da Sadiq Zazzabi

Ana ce-ce-ku-ce kan wasu hutuna da fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Maryam Booth ta wallafa na bikin aure.

Jarumar ta wallafa hotunanta tare da Sadiq Zazzabi mawakin Hausa kamar ango da amarya, hutunan da ke nuna kauna da soyayya.

Hutunan sun ja hankali mabiyanta da ma’abota finafinan hausa.

An ta yada hutunan a shafukan sada zumunta na intanet cewa Maryam Booth za ta yi aure.

Wasu na tunanin a fim ne, yayin da wasu ke cewa da gaske ne za ta auri Sadiq Zazzabi ganin cewa mawaki ne da ba ya fitowa a fim.

BBC ta tuntubi Maryam Booth domin tabbatar da ko da gaske ne za ta auri Sadiq Zazzabi.

Ban yi aure ba, a fim ne, in ji ta.

Ta kara da cewa an dauki hotunan ne a wani fim mai suna Gidan Biki na hudu da suka fito tare da mawakin.

More from this stream

Recomended