DA ƊUMI-ƊUMI: DSS sun cafke Sowore a filin jirgin na Legas

Jami’an Hukumar Ƴansandan Farin-kaya ta DSS sun kama Omoyele Sowore, jagoran kungiyar  #RevolutionNow Movement da ke adawa da gwamnati a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

Jami’an sun tsare Sowore, wanda shi ne mai jaridar yanar gizo ta Sahara Reporters, a yau Lahadi jim kaɗan bayan ya sauka a filin jirgin saman.

Kafin ya saukar, wasu ƙungiyoyin gwagwarmaya sun yi wa filin jirgin saman tsinke domin tarbar sa yayin da ya ke dawowa daga Amurka shi da iyalin sa.

Rahotanni sun baiyana cewa tun ranar Alhamis a ka fitar da bayanin umarnin kama Sowore idan ya dawo kasar, inda ya yi alla-wadai da hakan ya kuma jaddada aniyarsa ta dawowa Nijeriya.

More from this stream

Recomended