
Na’urarku na da matsalar sauraren sauti
Shugaban Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira ga al’umma su bi umarnin likitoci su daina musabaha domin kauce wa kamuwa da cutar cononavirus.
Malamin addinin Musuluncin ya shaida wa BBC haka ne bayan sanarwar da suka fitar ta jinkirta taron Maulidin Sheikh Nyass wanda da za a yi a Abuja da Sokoto saboda yaduwar cutar coronavirus.
Sheikh Dahiru Bauchi ya ce an jinkirta Maulidin ne saboda yadda cutar ke yaduwa a makwabtan Najeriya, kuma taron maulidin ba na ‘yan Najeriya ba ne kawai, har da ma ‘yan wasu kasashe.
Ya ce ba za a yi taron ba har sai annobar ta lafa a duniya sannan a sanar da ranar da za a gudanar da taron.
- Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar coronavirus
- Coronavirus: Yadda garkuwar jiki ke yakar cutar
“Abin da zan fada wa al’uma shi ne su saurari abin da likitoci suke fada; suke bayar da nasiha ko wanke hannu ko hana gaisawa da musabaha da mutane domin Allah ya ce ‘wanda ya san abu da wanda bai san shi ba ba za su zama daidai ba,” a cewar Sheikh Dahiru Bauchi.
Ranar Laraba hukumomin lafiya a Najeriya suka ce an samu karin mutum biyar masu dauke da coronavirus a kasar.
Hakan na nufin yanzu mutum takwas ne aka tabbatar suna dauke da cutar a Najeriya.
Kazalika gwamnatin Katsina ta ce an samu wani mutum da ake zargi ya kamu da cutar, ko da yake yanzu ana can ana yi masa gwaji domin gano hakikanin abin da ya faru da shi.
Gwamnonin jihohin arewa maso yammacin Najeriya sun ce za a rufe dukkan makarantu a jihohin saboda fargabar cutar ta coronavirus.