
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Saudiyya ta sanar da dakatar da mazauna kasar daga yin aikin Umrah na wucin gadi a kokarin kasar na hana yaduwar Coronavirus.
Wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta kasar ta fitar wacce kamfanin dillancin labaran Saudiyyar SPA, ya wallafa a shafinsa na intanet, ta ce an dauki wannan matakin ne domin bayar da hadin kai ga hukumomin lafiya na duniya don shawo kan cutar.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan ya danganta daukar matakin da kaguwar gwamnatin Saudiyyan na goyon bayan kokarin da duniya ke yi, musamman ma manyan hukumomi irin Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, na hana yaduwar cutar.
Amma sanarwar da aka fitar a ranar Laraba ta ce dakatarwar yin Umrar ta dan lokaci ce, kuma hukumomi za su ci gaba da nazari sannan za su janye matakin da zarar dalilan dakatarwar sun kau.
Sanarwar ta ce: ”Matakin dakatar da aikin Umrah ga mazauna kasar kari ne kan matakin gwamnati na dakatar da shigar baki masu ibadah Makkah da ziyara zuwa Masallacin Annabi a Madina, da kuma dakatar da shigar masu yawon bude ido daga kasashen da Coronavirus ta fi muni.”
Kazalika mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan ya kara da cewa daukar matakin ya zama wajibi ne saboda a takaita yaduwar annobar daga shiga manyan masallatan biyu masu tsarki, wadanda miliyoyin mutane ke shigar su.
A ranar Litinin 2 ga watan Maris ne Saudiyya ta tabbatar da samun bullar cutar Coronavirus a karon farko a kasar a jikin wani dan kasar da ya koma kasar daga Iran.
A hannu guda kuma, Ministan Lafiya na kasar Dr. Tawfiq bin Fawzan Al-Rabiah, ya tabbatar da cewa sakamakon gwajin da aka yi mutum 51 da suka yi cudanya da mai dauke da cutar ya nuna cewa ba sa dauke da ita.
Sai dai ya ce ma’aikatarsa ta lafiya tana jiran sakamakon gwajin sauran mutum 19 din.