Dan kwallon Brazil, Ronaldo Luis Nazario de Lima, ya kira tsofoffin abokan wasansa na Real Madrid ta na’urar bidiyo kai tsaye a shafinsa na Instagram.
Wadanda ya kira din su ne David Beckham, Luis Figo, Roberto Carlos da kuma Iker Casillas.
Ronaldo ya kira su daya bayan daya domin sada zumunci.
David Beckham da alakarsa da Brazil
Beckham ya shafe shekaru hudu a Real Madrid daga shekarar 2003 zuwa 2007, inda ya lashe kofin La Liga da kuma Super Cup.
A lokacin hirarsu, Ronaldo ya shaidawa Beckham cewa yana daga cikin manyan ‘yan wasan tsakiya a duniya.
“Yadda kake sarrafa kwallo, ka aika ta ba tare da ka kalli wurin ba, abin sha’awa ne,” in ji Ronaldo.
Sun yi maganar coronavirus da Roberto Carlos
Carlos wanda dan kwallon baya ne na Brazil, ya lashe gasar La Liga hudu da na zakarun Turai uku a Real Madrid tun daga shekarar 1996 zuwa 2007.
Sun yi maganar yadda tsohon shugaban Real, Lorenzo Sanz ya mutu saboda kamuwa da cutar Coronavirus.
Sanz ne ya siyo Carlos a Real.
Tuna baya tare da Luis Figo
Kamar Ronaldo, Figo ya murza a Barcelona da kuma Real Madrid.
Figo ya ce “lokacin da muke buga kwallo a tare, mun samu nasarori sosai”.
Figo ya lashe kofin La Liga biyu tare da Real Madrid sannan ya ci kofin zakarun Turai a 2002.