‘China ba za ta yadda a yi mata mulkin-mallaka ba’ inji Xi Jinping

Shugaban kasar Chana Xi Jinping

Shugaban China Xi Jinping, ya sha alwashin cewa kasar sa ba za tayi amfani da wasu kasashe domin ci gaban ta ba.

Ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi a wajen bikin cika shekara 40 da kasar ta kawo manyan sauye- sauya a fannin tattalin arziki.

Ya kuma bayyana cewa kasarsa ba za ta amince wasu kasashe su juya ta ba.

Tsarin tsohon shugaban kasar Deng Xiaoping na son kawo “gyara” ya fara ne shekara 40 da suka wuce.

Shekara 40 ke nan tun bayan aikata sauye-sauye a kan tattalin arzikin kasar
Wadannan gyare-gyare sun mayar da kasar a yanzu ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Tsarin ya fitar da miliyoyin mutane daga talauci, amma a kwanakin baya Chana tana fama da bashi da kuma raguwar habbakar tattalin arziki.

More from this stream

Recomended