Buhari ya ziyarci sojojin da suka jikkata a yaki da Boko Haram

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ya kai ziyarar jaje g sojojin da suka samu raunuka a yakin da suke da yan ta’addar Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Shugaban kasar ya ziyarci sojojin ne a wani bangare na ziyarar da ya kai Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Buhari ya yabawa sojojin kan yadda suke nuna jarumtaka a yakin da suke na kare kasarnan daga hare-haren yan ta’addar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasarnan.

Ya kuma jinjina musu a madadin dukkanin yan Najeriya kana ya yi addu’a ga waɗanda suka riga mu gidan gaskiya.

Ziyarar ta Buhari zuwa birnin Maiduguri na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan da yan kungiyar Boko Haram suka kai wani mummunan farmaki kan wani sansanin sojoji dake Metele a jihar ta Borno inda suka kashe soja sama da 100.

More from this stream

Recomended