
Buhari ya tura babban hafsan sojin sama zuwa Zamfara da Sokoto
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen mutane da aka yi a kananan hukumomin Birnin Magaji da Tsafe da Maradun da wasu yankuna na jihar Zamfara.
Wata sanarwar da kakakin Shugaban na Najeriya Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce dole ne a kawo karshen kashe-kashen wadanda ya kira munanan laifuka kan bil’adama.
Ya jajantawa iyalan wadanda aka kashe da kuma mutanen Zamfara.
Ya kuma umurci babban hafsan sojin sama Air Marshall Abubakar Baba Sadiq ya kai ziyara Zamfara da sokoto da sauran jihohin da ke fama da matsalar ‘yan bindiga da ‘yan fashi da makami da kuma masu garkuwa da mutane.
Duk da sojoji da ‘yan sanda da aka tura a Zamfara, amma har yanzu al’ummar jihar na cewa babu wani sauki ga matsalar tsaron da suke fuskanta.
Damuwa da yawan kashe-kashe ne ya sa wasu al’ummar Zamfara a karamar hukumar Tsafe suka kaddamar da zanga-zanga.
Akalla mutum uku ‘yan sanda suka ce an kashe, yayin da suka ce sun kama mutum 23 daga cikin masu zanga-zangar da suka kira ta “masu zaman banza.”
Rahotanni sun ce matasa da ‘yan gudun hijira da suka kunshi mata da yara kanana sun toshe babbar hanyar da ke zuwa Gusau, tare da kone wasu gine-ginen gwamnati.
Mazauna garin na tsafe na bayyana damuwa ne kan yadda masu gudun hijira ke ci gaba da tururuwa a yankin, suna guduwa sakamakon hare-haren da ake zargi yan bindiga da barayin shanu ke kai wa.
Shugaban karamar hukumar Tsafe Alhaji Abubakar Aliyu ya shaida wa BBC cewa, sama da mutum 40 ne suka rasa rayukansu a kauyuka daban-daban cikin mako biyu.
A yanzu dai ana ganin yadda rikici ke kara bazuwa da karuwa kuma ga alama ba a san hanyoyin da za a bi a shawo kansa ba.
Abun da yake a bayyane kawai shi ne yadda dumbin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ke ci gaba da mutuwa.
Gwamman mutane sun mutu a ‘yan watannin da suka gabata sakamakon hare-haren da aka kai wasu kauyuka a jihar Zamfara.
Sai dai saboda rashin isassun maso kawo bayanai, zai yi wahala a fadi adadin mutanen da suka mutu a rikicin da aka shafe shekara shida ana yi.
A tsawon shekarun da suka gabata ana ci gaba da samun matsalolin satar mutane don kudin fansa da kuma fyade a wasu kauyuka na jihar Zamfara.