Buhari ya roki yan Najeriya su kara bashi lokaci

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya nemi yan Najeriya da su bashi isasshen lokacin domin ya aiwatar da tsare-tsaren da yake da su akan Najeriya.

Buhari ya fadi haka bayan wani faretin ban girma na musamman da sojojin dake fadar shugaban kasa suka gudanar domin bikin cikarsa shekaru 76

Shugaban kasa wanda yake cikin farin ciki da raha ya tambayi dan jarida dalilinsa na rage masa shekaru.

“Me yasa zaka rage mini shekaruna da shekara daya,’shugaban kasar ya tambaya.

Ya yi kira ga yan Najeriya da su cigaba da yi masa addu’a dama kasa baki daya inda ya neme su da su cigaba da samun karin fahimta kan manufofi da tsare-tsaren gwamnatinsa da za su kawo cigaban ƙasa.

“Yakamata yan Najeriya su cigaba da yimini addu’a su kuma fahimci aniyata kana su bani lokaci,” ya ce.

Ya ce gwamnati zata cigaba da tunatar da yan Najeriya nasarorin da ta samu cikin shekaru uku da rabi.

More from this stream

Recomended