Buhari ya mayar wa PDP martani

[ad_1]

Buhari Sallau

Hakkin mallakar hoto
Facebook/ Nigeria Presidency

Image caption

Shugaban ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC da kuma wadansu ‘yan majalisa a gidansa da ke Daura

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar wa jam’iyyar PDP martani, inda ya ce gwamnatinsa na bakin kokarinta wajen magance manyan kalubalen kasar.

Ya ce maganganun da jam’iyyar take yi game da gwamnatinsa ba za su “kawar da hankalin gwamnatinsa daga ci gaba da ayyukan alherin da take yi ba.”

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin wata liyafa da wandansu gwamnonin jam’iyyar APC da kuma wadansu ‘yan majalisa a gidansa da ke Daura ranar Alhamis.

A watan jiya ne Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da wadansu gwamnoni da kuma ‘yan majalisa suka sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

Har ila yau Shugaba Buhari kara jaddada cewa jam’iyyar APC ta fahimci kalubalen da kasar take fuskanta, inda ya bukaci goyon bayan al’ummar kasar wajen magance su.

“Muna farin ciki idan muka fahimci cewa jama’a na jin dadin ayyukan da muke yi. Kuma muna sane da alkawurran da muka yi lokacin zaben 2015. Ba mu kawar da hankalinmu daga kansu ba,” in ji shi.

Daga nan ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai kan tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

“Ko ‘yan adawa ba za su dora mana laifi ba game da kokarinmu wajen gyara wadannan matsalolin.”

“Za mu ci gaba da yin bakin kokarinmu a wannnan shugabancin da Allah Ya ba mu kuma muna godiya kan goyon bayan da jama’a suke ba mu,” in ji shugaban.

[ad_2]

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...