Buhari ya mayar wa Obasanjo da Atiku martani

Buhari


Obasanjo ya goyi bayan Buhari a zaben 2015, amma yanzu ya ce baya goyon bayan takararsa a zaben 2019

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar wa tsohon Shugaban kasar Olusegun Obasanjo martani game da nuna goyon bayansa ga Atiku Abubakar a zaben 2019.

A ranar Alhamis ne dan takarar shugabancin kasar a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya gana da Mista Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta a jihar Ogun, inda rahotanni suka ce ya ce yana goyon bayan Atikun a zaben 2019.

Sai dai a wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaba Buhari kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ba su yi mamakin labarin da ke cewa “Obasanjo yana goyon bayan a Atiku a zaben 2019, dukansu ba za su yi nasara ba.

“Ba mu manta ba kuma ‘yan Najeriya su ma suna sane cewa kimanin shekara 11 da ta wuce ne tsohon shugaban da kuma tsohon mataimakinsa a kokarinsu na neman mulki suka zargi juna da aikata cin hanci da karbar rashawa,” in ji Malam Garba Shehu.

Atiku Abubakar ya wallafa hotunansa a shafinsa na Twitter tare da Obasanjo da malamin addinin Musulunci Dr Ahmad Gumi da malamin addinin Kirista Bishop Matthew Hassan Kuka.


Atiku ya gana da Cif Olusegun Obasanjo da Sheikh Ahmad Gumi da Bishop Matthew Hassan Kukah a ranar Alhamis

Atiku Abubakar ne ya yi wa Olusegun Obasanjo mataimaki lokacin da yake shugaban najeriya tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.

Tun bayan nan, dangantakar da ke tsakaninsu ta yi tsami kuma Obasanjo bai taba goyon bayan Atiku Abubakar ba a duk lokutan da ya fito a baya na nuna son yin shugabancin Najeriya.

An taba ruwaito Obasanjo yana cewa “zai yi iya bakin kokarinsa don ganin Atiku Abubakar bai shugabanci Najeriya ba.”

Sai dai a wata hira da BBC ta yi da Atiku Abubakar, ya ce “Obasanjo ba shi ne Allah ba, kuma ba shi ne mutanen Najeriya ba.”

Olusegun Obasanjo dai na daya daga cikin masu fada a ji a fagen siyasar Najeriya.

Kuma ya nuna goyon bayansa ga Shugaba Buhari a lokacin da ya lashe zaben 2015, sai dai a bana ya ce ba ya goyon bayan shugaban ya nemi wa’adi na biyu a zaben shekarar 2019.

More from this stream

Recomended