Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdul Samad Rabiu, ya bayyana cewa kamfaninsa zai ci gaba da rage farashin shinkafa da sauran kayan abinci a Najeriya, yana mai cewa farashin ya fara sauka tun shekarar da ta gabata.
Rabiu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, jim kaɗan bayan ganawarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
A cewarsa, matakin Shugaba Tinubu na bayar da damar shigo da wasu kayan abinci daga ƙasashen waje ba tare da karɓar harajin fito ba, ya taimaka ƙwarai wajen karyewar farashin kayan masarufi a ƙasar.
“Wannan matakin gwamnati mataki ne mai kyau, kuma yana da tasiri sosai wajen tabbatar da saukin rayuwa. Wannan shi ya ba kamfanonin sarrafa abinci damar shigo da kaya cikin sauƙi,” in ji Rabiu.
A watan Yuli na shekarar 2024 ne gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da karɓar kuɗin fito daga kan kayan abinci da ake shigowa da su daga waje, domin takaita hauhawar farashin kayayyaki.
Shugaban kamfanin BUA ya kuma zargi wasu ‘yan kasuwa da sayen kayan abinci domin ɓoyewa, inda daga bisani su fito da su suna sayarwa da tsadaddan farashi ga kamfanonin sarrafa abinci.
“Wasu suna ɓoye shinkafa da sauran kayan abinci har na tsawon watanni uku, domin su hana samuwa a kasuwa sannan su sayar da su da tsada. Amma da zarar kamfanonin suka shigo da kaya masu yawa, dole suka fito da nasu kayan suna sayarwa a farashi mai sauƙi,” in ji shi.
Rabiu ya ƙara da cewa kamfanonin BUA za su ci gaba da goyon bayan wannan mataki na gwamnati domin ganin an samu saukin farashin abinci a kasuwa.
“Za mu ci gaba da rage farashin kayan abinci domin tallafa wa jama’a, kuma ina da tabbacin cewa farashin zai ƙara sauka nan gaba,” in ji shi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ya nuna cewa an samu saukin farashin kayayyaki a watan Afrilu idan aka kwatanta da watan Maris.
‘BUA zai sake rage farashin shinkafa da sauran kayan abinci’
