Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya karyata jita-jitar cewa ya bar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya koma hadakar adawa ta African Democratic Congress (ADC).
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Mustapha ya bayyana labarin a matsayin ƙarya, yana mai cewa bai taɓa yin wata tattaunawa da jam’iyyar adawa ko abokan haɗin gwiwar su ba.
“An ja hankalina kan wani labari da ke danganta ni da hadakar adawa da kuma zaben ADC a matsayin jam’iyyarsu. Ina so jama’a su sani cewa wannan labari ƙarya ne. Ba ni cikin kowace hadakar adawa kuma ba na tattaunawa da waɗanda ke ciki,” in ji shi.
Ya ce yana daga cikin manyan wadanda suka kafa jam’iyyar APC, don haka ba zai iya barin jam’iyyar da ya taimaka wajen kafa ta ba. Ya kuma jaddada cewa duk da cewa APC na da ƙalubale kamar kowace jam’iyya, mafita ita ce a yi aiki daga ciki, ba tare da komawa wani sabon dandalin siyasa ba.
Ya roki jama’a da su yi watsi da duk wata jita-jita da ta saba da wannan bayani.
Mustapha ya yi aiki a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya daga 2017 zuwa 2023.
Boss Mustapha Ya Musanta Ficewa Daga Jam’iyyar APC
