
Wasu rahotanni na cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun samu nasarar kwace garin Baga dake jihar Borno inda suka kafa tutarsu a garin.
Wani mazaunin garin ya fadawa jaridar The Cable da yammacin ranar Alhamis cewa yan ta’addar sun samu nasarar kwace garin bayan da suka yi nasarar kwace sansanin sojojin rundunar kasa da kasa dake garin.
“Bayan da suka fatattaki sojoji sun raba wasu mutane da gidajensu sun kuma kafa tutarsu,”babu wanda ya isa ya musalta faruwar haka a cewar wani mazaunin garin da ya nemi a boye sunansa.
Wani mazaunin garin mai suna, Labbo Dan-Baga ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da ya yi da shirin wani gidan Rediyo da jaridar ta The Cable ta bibiya.
“Boko Haram sun kafa tutarsu a Baga mun tafi masallaci yin sallah sai muka gano ashe a kewaye muke da mayakan Boko Haram,”
“Sun fada mana kada mu tsorata ya yin da muka yi salla tare da su, sun ce baza su kashe farar hula ko daya ba kuma su ya’yan kungiyar Boko Haram ne dake biyayya ga Albarnawi sun fada mana zamu iya zama a garin ko kuma mu fita,” ya ce.
Wata majiyar ta bayyana cewa yan ta’addar sun fafata da sojoji a garuruwan Doron Baga, Cross Kauwa da kuma Kukawa dake jihar ta Borno inda suka samu nasarar kwace motoci da dama dake dauke da bindiga.