A lokacin shayarwa ne ake samun alaka ta shakuwa da kauna da jituwa a tsakanin mahaifiya da jaririnta.
Likitoci sun bayyana cewa, akwai hanyar da ta dace uwa ta rike jaririnta, don ta shayar da shi kamar yadda ya kamata.
Akwai wasu hanyoyi da ake bi a likitance, wajen shayar da jariri cikin sauki kamar haka:
- Na farko mai jego za ta dora jariri a kan cikinta, ta yadda za ta hada cikinsa da nata.
- Mace za ta dago yaro, ya taho ga nononta, ba ita ya kamata ta sunkuya don ta kai nono ga jaririn ba.
- Sai ta sanya kan jariri a kan hannunta, ta hakan zai zama idonsa yana kallonta.
- Sai ta fara shayar da shi ruwan nono.
Rashin rike jariri kamar yadda ya kamata wajen shayarwa, a kan janyo uwa ta gani da wuri, musamman masu haihuwar fari. In ji likitoci
Yayin da ya kan janyo wa wasu matan ciwon baya da fargaba da dai sauransu.
Karin wasu matsalolin da mata kan fuskanta wajen shayarwa sun hada da karancin ruwan nono, ko kuma tsagewar kan nono ko ma rashin fitowar kan nono kamar yadda ya kamata.
To domin jin karin wasu bayanai kan yadda ya kamata mace ta yi shayarwa kuma ta kaucewa matsalolin da muka zayyana da ma wasu, sai ku latsa shirin lafiya zinariya da ke sama.