
Toshon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa ya musalta rahoton da wasu mutane ke yadawa cewa zai fice daga jam’iyar PDP.
Wasu mutane ne suke yada jita-jitar cewa tsohon gwamnan kuma sanata a majalisar dattawa dake wakiltar mazabar Kano ta tsakiya ya shirya tsaf domin barin jam’iyarsa ta PDP.
Kwankwaso ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Sakon ya bayyana cewa wasu kalamai na yawo a kafafen sadarwar zamani dake cewa zan fita daga jam’iyar PDP.
Tsohon gwamnan ya nesanta kansa daga waccan kalaman karya da ake yadawa inda ya ce haryanzu shi dan jam’iyar PDP ne kuma zai cigaba da zama a cikinta daram- dam ba tare da fita daga ciki ba.