Babu hannun gwamnatin Yobe wajen zubar wa mata ciki – NHRC

Hukumar Kare Haƙƙin Bil-adama ta Najeriya, NHRC ta ce babu hannun gwamnatin jihar Yobe a zargin da rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi na cewa gwamnatin ta haɗa baki da sojoji wajen zubar wa da mata ciki a asirce.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na Tuwita, gwamnatin jihar Yoben ta ce wannan zargi abu ne da tunani ko hankali ma ba zai ɗauka ba.

Cikin watan Disamban 2022 ne dai kamfanin dillanci labarai na Rueters ya wallafa wani rahoto, inda ya zargi sojojin Najeriya da hannu wajen zubar wa da mata akalla 10,000 ciki a asirce.

Kwamishinan shari’a na jihar Saleh Samanja ne ya bayyana haka ga kwamitin bincike na ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama a lokacin da suka ziyarci jihar.

Don gudanar da bincike kan zarge-zargen take haƙƙin bil adama a yankin arewa maso gabashin ƙasar,

Kwamishinan ya ƙara da cewa babu wata gwamnati da za ta yadda a haɗa baki da ita wajen kashe mata da ƙananan yara da sunan kore tsangwamar da suke fuskantar na kasancewa da ‘yan Boko Haram.

More from this stream

Recomended