Babbar mai shari’a a Kenya na fuskantar shari’a

[ad_1]

Mataimakiyar babban mai shari’a kasar Kenya za ta sake gurfana gaban kotu domin fuskantar tuhuma kan rashawa da cin hanci da kuma kaucewa biyan haraji.

Mai shari’a Philomene Mwilu, ita ce ta biyu mafi girman mukami da ake tuhuma a yakin da gwamnatin kasar ke yi da rashawa.

Za ta sake gurfana ne gaban kotu ranar Laraba bayan bayar da belinta a jiya Talata da aka kama ta.

Babban mai shigar da kara na kasar Kenya Noordin Haji, ya ce akwai hujjoji da suka tabbatar da tuhumar da ake yi wa mai shari’a Mwilu.

Ya ce: “hujjojin da muke da su sun bayyana cewa, na farko, mai shari’a Mwilu ta karya ka’idojin aiki domin bukatun kanta, ta karbi kudi a matsayin kyauta ya cin mutunci ne ga ofishinta da kuma kaucewa biyan haraji. Don haka wadannan hujjoji ne da suka isa a amince da laifukan da ake tuhumarta” in ji shi.

Philomena Mwilu, tana cikin manyan masu shari’a guda bakwai a kotun koli da suka soke zaben farko na shugaban kasa da Uhuru Kenytatta ya lashe a watan agustan 2017, matakin da ya sa aka sake zaben.

Hukuncin Kotun ya fusata Shugaba Uhuru Kenyatta wanda ya sha alwashi yin kwaskwarima a bangaren shari’a.

Mista Haji ya musanta zargin cewa shari’ar da ake kan Mwilu na da nasaba da siyasa, yana mai cewa mataki ne mai zaman kansa.

Ya ce suna aiki ne dari bisa dari bisa kudin tsarin mulki ba wai don biyan bukatar mutum guda ba, kuma za su yi amfani da wannan dama domin tabbatar da adalci a bangarorin gwamnati.

[ad_2]

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...