Baya ga majalisar dokokin, kungiyar lauyoyin ta shigar da kara ga Atoni Janar kuma kwamishinan shari’a na Kano kana da shugaban kwamitin da majalisar dokokin ta kafa na bincikar wannan batu na rashawa a kan gwamnan Kano.
Barrister Mohammed Ma’aruf shine lauyan dake bada kariya ga gwamna Ganduje a gaban kwamitin bincike na majalisar.
Ko me wadannan lauyoyin rajin demokaradiyya ke muradin cimmawa har suka tafi kotu? Barrister Zubair ya bada karin haske akai
Sai dai duk da haka majalisar dokokin ta ce bata da masaniyar wannan kara a hukumance. Hon Baffa Babba DanAgundi shine shugaban kwamitin binciken da majalisar keyi.
A baya dai yau ne talata majalisar dokokin ta Kano ta tsara fara aikin tantance faifen bidiyon zargin rashawar dala miliyan 5 akan gwamna Ganduje daga hannun ‘yan kwangila.