Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Dr. Babachir David Lawal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki, a daidai lokacin da ake kara samun tashin hankali a cikin jam’iyyar, musamman daga yankin Arewa.
Babachir ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na mazabar Bangshika a karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa. Wasikar mai taken “Wasikar Ficewa Daga Jam’iyyar APC” ba ta bayyana dalilin ficewar ba, sai dai an san cewa tsohon Sakataren Gwamnatin yana da sabani da shugaban kasa Bola Tinubu tun lokacin da aka zabi tikitin musulmi da musulmi kafin zaben 2023.
Duk da ficewarsa daga APC, Babachir ya ce bai shiga wata sabuwar jam’iyya ba a halin yanzu. Ya ce zai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai shiga a gaba, inda zai hada kai da wasu ‘yan kasa domin ciyar da Najeriya gaba.
Ficewar wannan fitaccen dan siyasa na daga cikin alamomin da ke nuna yuwuwar rugujewar jam’iyyar APC kafin babban zaben 2027, duba da yadda rashin jituwa ke kara kamari tsakanin mambobinta, musamman daga yankin Arewa.
A baya-bayan nan ne dai wani hadin gwiwa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ke jagoranta ya amince da amfani da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin dandali domin
Babachir Lawal Ya Fice Daga Jam’iyyar APC, Ya Yi Barazana Ga Makomar Jam’iyyar Kafin Zaben 2027
