Babachir Lawal: Tinubu Ya Min Ba Daidai Ba, Kuma Yana Da Girman Kai

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce shi bai yi wa Shugaba Bola Tinubu ba daidai ba, sai dai a maimakon haka, Tinubu ne ya cutar da shi.

Lawal ya bayyana haka ne a shirin Politics Today na tashar Channels Television a ranar Litinin, lokacin da yake amsa tambayoyi daga mai gabatarwa, Seun Okinbaloye.

Da aka tambaye shi ko har yanzu abokai suke da Tinubu, Lawal ya ce:
“Eh, tabbas, abokai muke. Ya kamata ka iya gaya wa abokinka gaskiya ko a gaban talabijin na kasa. Karon karshe da na yi magana da shi (Tinubu) shi ne watan Yuli, 2022.

“Matsalar Bola Tinubu ita ce yana tunanin na cutar da shi. Ni ban cutar da shi ba. Amma shi ne ya cutar da ni. Kuma yana cike da girman kai saboda yana ganin shi ne wai shugaban kasa.”

More from this stream

Recomended