
Wani jigo a tafiyar Atiku Abubakar, dan takarar shugabancin Najeriya a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Injiniya Gambo Bichi, ya shaida wa BBC cewa, su ba su taba ganin irin wannan abun ya faru ba a Najeriya a ce an binciki dan takarar shugabancin kasa a babbar jam’iyya adawa, sannan kuma tsohon mataimakin shugaban kasa a filin jirgin sama ba.
Ya ce ba shakka wannan abu da aka yi wa uban gidansu tamkar karan tsaye ne a dimokradiyya.
Engr Gambo Bichi, ya ce ita kanta jam’iyyarsu ta PDP, da ma magoya bayanta sam basu ji dadin wannan abu da ya faru ba domin tamkar kamar cin fuska ne.
A safiyar ranar Lahadi ne Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa jami’an tsaron kasar sun bincike shi jim kadan da isarsa Abuja, babban birnin tarayyar kasar.
Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya koma kasar ne daga birnin Dubai inda ya shafe kwana da kwanaki tare da wasu abokan siyasa da mukarrabansa.
To Sai dai kuma wasu kafofin yada labarai a Najeriyar sun ambato ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, na cewa jami’an hadin-gwiwa kan safarar kudi sun binciki tsohon mataimakin shugaban kasar ne kamar yadda suka saba, kuma sun bai wa Atiku Abubakar cikakkiyar girmamawa a matsayinsa na babban dan kasa.