Ayyukan Da Tinubu Ke Yi Ne Suka Sa Ƴansiyasa Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyyar APC—A Cewar Gwamna Sule

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana cewa ci gaban da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke samu ne ke janyo mutane daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan wata ganawa ta sirri da Tinubu.

“Ina ganin mutanen da ke farin ciki da abin da suke gani su ne ke dawowa jam’iyyar. Wannan kuwa alamar nasara ce ga shugaban ƙasa da jam’iyyar APC gaba ɗaya,” in ji Sule.

Ya ce sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa – irin su daidaita farashin canjin kuɗi, cire tallafin mai, da gyaran ɓangaren wutar lantarki – su ne ke ƙara wa jam’iyyar karɓuwa a idon jama’a. Haka kuma, ya jaddada mahimmancin tsarin koyon sana’o’i da bunƙasa noma.

Gwamnan ya ƙaryata zargin da wasu ‘yan adawa ke yi cewa Najeriya na ƙarkata zuwa tsarin jam’iyya guda. A cewarsa, “Babu yadda za a yi Najeriya ta zama ƙasa da jam’iyya guda. Amma muna fata mu kasance jam’iyyar da tafi ƙarfi, ba lallai mu mallaki komai ba.”

Ya kwatanta tsarin da na Amurka inda jam’iyyu biyu suka fi karfi, amma ƙananan jam’iyyu har yanzu na ci gaba da taka rawa.

A wani bangare na jawabin nasa, Gwamna Sule ya bayyana ci gaban da ake samu wajen samar da baturin Lithium a jiharsa. Ya ce an kaddamar da wani katafaren kamfani da ke iya sarrafa tan miliyan uku a shekara, yayin da wani kamfani mafi girma zai fara aiki nan da watanni biyu.

More from this stream

Recomended