Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana kisan da aka yi wa sama da mutum 200 a wasu ƙauyuka na jihar Benue a matsayin abin kunya da kuma alamar ƙara tabarbarewar tsaron Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Atiku ya bayyana alhinin da ya shiga saboda kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba. Ya ce, “Wannan hari da aka kai wa ‘yan Najeriya ba kawai masifa ce ta wani yanki ba; wata gaggautacciyar matsala ce ta ƙasa baki ɗaya da ke bukatar hanzari da tsauraran matakai.”
Ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta jihar Benue da su gudanar da cikakken bincike mai adalci da gaskiya kan lamarin, tare da kamo masu hannu a cikin wannan danyen aiki domin su fuskanci hukunci. Haka kuma, ya ce dole ne a ƙara ƙaimi wajen ɗaukar matakan tsaro domin hana sake afkuwar hakan.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada bukatar tura jami’an tsaro masu isasshen kayan aiki zuwa yankunan da ke fama da barazana, tare da inganta tattara bayanan sirri da kare al’ummomi, musamman a yankunan karkara.
Har ila yau, Atiku ya nemi a gaggauta ba wa waɗanda suka tsira daga harin tallafi, wanda ya haɗa da kulawar lafiya, taimakon rage radadin tashin hankali, da kuma tallafa musu wajen farfaɗo da rayuwarsu.
Ya ce, “Zuciyata da addu’o’ina na tare da duka iyalan da abin ya shafa da kuma al’ummomin da suka rasa masoyansu, gidajensu da kwanciyar hankalinsu. Babu kalmomin da za su iya bayyana girman raɗaɗin da suka fuskanta.”
Atiku ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina kallon abubuwa ta fuskar kabila da addini, su haɗa kai don neman gaskiya da zaman lafiya mai dorewa.
Ya ƙara da cewa, “Mu tashi tsaye a matsayin ƙasa guda wajen Allah-wadai da irin waɗannan muggan ayyuka. Allah Ya jikan waɗanda suka rasa rayukansu, Ya ba da lafiya ga waɗanda suka jikkata, Ya kuma dawo da zaman lafiya a ƙasarmu.”
Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Kisan Gilla A Benue, Ya Ce Wannan Musiba Ce Ta Ƙasa Baki Ɗaya
