Atiku ya taya Buhari murnar cika shekaru 76

Tsohon mataimakin shugaban kasa,Atiku Abubakar kuma mai neman zama shugaban kasar Najeriya a shekarar 2019 a karkashin jam’iyar PDP ya taya shugaban kasa, Muhammad Buhari murnar cika shekaru 76 da haihuwa.

A ranar Litinin 17 ga watan Disamba shekarar 2018, shugaban kasa Muhammad Buhari ya cika shekara 76 da haihuwa.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya taya shugaban ƙasar murnar zagayowar wannan rana.

Haka kuma dantakarar na jam’iyar PDP ya bayyana cewa shi da shugaban kasa Muhammad Buhari yan uwan juna ne domin uwa daya ce ta haifesu wato Najeriya.

Sakon ya ce,””Ina taya Shugaba @MBuhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa, kuma ni da iyalina muna masa addu’ar tsawon rai. Duk da cewa ni da shi za mu hadu a fagen zabe nan ba da jimawa ba, ina so na tabbatar da cewa ni da shi ‘yan uwan juna ne da muka fito daga mahaifa daya wato Najeriya.”

More from this stream

Recomended