Asalin wakar Hamisu Breaker da ta sa matan aure gasar rawa

Hamisu Breaker

Hakkin mallakar hoto
Alamy

Image caption

‘Idan zan yi waka ba na tunanin samari da ‘yan mata kawai’

Tun bayan da bidiyon gasar rawar matan aure ya zama ruwan dare gama duniya a arewacin Najeriya da aka yi lokacin bikin sallah, sai hankalin mutane ya koma kan wakar da ta sa suka taka rawar.

Wannan waka dai takenta shi ne ‘Jarumar Mata’ wadda Hamisu Breaker Dorayi ya rera.

Duk da cewa mawakin ya ce ya yi wakar ne a karshen shekarar 2019, kuma ya sake ta a farkon 2020, za a iya cewa dubban mutane ba su san ta ba sai a makon bikin karamar sallah, bayan da wasu matan aure suka yi yayin yin rawarta.

A wata hirar bidiyo kai tsaye da BBC Hausa ta yi da Hamisu Breaker a shafinta na Instagram, matashin mawakin ya ce wannan gasa da mata suka yi ba karamin farin jini ta kara masa shi da wakar ba.

Ya ce: ”Wakar ta yi matukar tashe a lokacin da ta fito amma na yi tunanin ma tashenta ya dan ja baya, kawai kwanan nan sai na ji ta sake karade duniya.”

Abin da ya sa na yi wakar

Hakkin mallakar hoto
Instagram/Hamisu_Breaker_Dorayi

Image caption

Breaker ya ce yana gab yin aure

”Abin da ya sa na yi wakar jarumar mata na yi duba ne kan mutane. Idan zan yi waka inda duba halayyar mutane ne, misali wani na da zurfafawa wajen soyayya wasu kuma ba su da.

”Kuma na ga na kwana biyu ban yi wa masoya waka ba, shi ya sa na ce bari nai musu. Ba budurwata na yi wa ba gaskiya.

” Idan zan yi waka ba na tunanin samari da ‘yan mata kawai, ina farawa ne tun daga kan tsoho mai shekaru da yawa, haka-haka har zuwa kan masu karancin shekaru yadda kowa zai ji wani abu da ya dangance shi.

Hamisu ya ce ya tsaya tsaf ne ya zabi kalaman da ya yi amfani da su a cikin wakar. ”Alal misali baitin farko da nake cewa ashe da rai nake sonki Jaruma ba da zuciyata ba. Kin ga hakan na nufin wannan soyayyar sai ranar da aka mutu za a daina ta tun da ba da zuciya mai sauye-sauye ake yin ta ba.

Na ji matukar dadi

To ko yaya Breaker ya ji bayan da wakar ta sake shahara a baya-bayan nan? ”Ban taba tsammanin wakar za ta zaburar da matan aure ba har su yi gasa a kanta. Na yi ne don masoyana da fatan ta shahara, sai kuma ga shi ta yi irin farin jinin da ban yi tsammani ba,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: ”A lokacin da na ga mata sun fara gasar sai na ji dadi sosai, na ce na zama daya daga cikin mutanen da suke ba da gudunmowa a cikin gyaran aure. Ban taba tunanin ganin haka ba gaskiya.

A ranar ina ta tunanin kamar na sanya bidiyon matan a shaina, amma kuma sai na yi tunanin hakan bai dace ba. Amma na ji dadi kuma na musu fatan alkhairi.

Breaker ya ce bai san adadin mutanen da suka kira shi a waya don sanar da shi cewa ya ga yadda wakarsa ta yi tashe a wannan dan tsakanin na bikin sallah ba.

BBC ta tambaye shi kan ra’ayinsa kan rawar matan aure a bidiyo a saka a shafukan sada zumunta.

Sai ya ce duk da dai a tunaninsa sanya rawar a social media din na iya zama kuskure. Amma tun da ni ba malamin addini ba ne ba zan iya fashin baki kan hakan ba.

Wakar Jarumar Mata

Wakar dai tana da baituka tara ne masu sadara hurhudu, kuma tana karewa da kafiya.

Hamisun ya ce baitin da ya fi so shi ne na bakwai da yake cewa:

”Yau ga ni a ruwa kusa da kasa zo ki cecei karkona

Komai da mafita ka da ki saba da furta bankwana

Ina ji in a gani yadda nake sonki ya fi karfina

Na san a duniya da wanda yake janye duk tunanina.

Wane ne Hamisu Breaker?

Hakkin mallakar hoto
Chizo Photography

Image caption

An haifi shahararren mawakin Hausan ne a shekarar 1993 a Kano

Sunansa Hamisu Breaker Dorayi, kuma dan asalin jihar Kano ne, shekarunsa 27.

Ya yi karatun firamare da sakandare a unguwar Dorayi. Ya fara waka tun yana makarantar Islamiyya lokacin yana yaro, amma a shekarar 2016 aka fara sanin sa.

Zuwa yanzu ya yi wakokin da shi kansa ya ce bai kirga yawansu ba.Ya yi wakoki irin su So, da SHimfidar Fuska da HAuwa da sauran su.

More from this stream

Recomended